News
WHO Ta Ce Akalla Yara Miliyan Daya Sun Samu Allurar Rigakafin Cutar Zazzabin Cizon Sauro Zagayen Farko A Nahiyyar Afirka
Advertisements

Daga Muhammad Muhammad zahraddin
Hukumar lafiya ta duniya WHO ta ce akalla yara miliyan daya a Afirka sun samu allurai daya ko fiye da haka na rigakafin cutar zazzabin cizon sauro zagayen farko a nahiyyar.
Hukumar ta kuma ce, an sanya kananan yara a Ghana, Kenya, da Malawi cikin wani sabon shirin yakar cutar.
Gigakafin cutar zazzabin cizon sauro, wanda gwamnatin Malawi ce ta fara kaddamar da shi a watan Afrilun 2019, ya nuna cewa maganin yana da lafiya kuma yana iya rage kaifin cizon sauro.
Advertisements
