News
APC ta bukaci ministocin Buhari da ke son yin takara su ajiye aiki
Daga maryam bashir musa
Domin kaucewa taka dokar zabe ta Najeriya, jam’iyyar APC mai mulkin kasar ta bayyana ranar karshe da ministoci da masu rike da mukaman gwamnati ya kamata su ajiye ayyukansu a matakan tarayya da na jihohi idan suna son tsayawa takara a zabukan da ke tafe.
Jami’an gwamnatin na da zuwa ranar Asabar 30 ga watan Afrilu su ajiye mukaman nasu.
Matakin ya shafi wasu ministocin gwanatin Buhari kamar ministan sufuri Chibuike Rotimi Amaechi da kwadago Chris Nigige, suna ciki jami’an da suka bayana aniyarsu ta tsayawa takara.
Sashe na 3(i) na dokar jam’iyyar APC kan tsayar da ‘yan takara a zaben 2023 na cewa: “Ba a yarda wani jami’in da ke rke da mukami a kowane matakin gwamnati ya zama deleget ko a zabe shi domin fitar da ‘yan takara.”
Jadawalin zabe da hukumar zabe mai zaman kanta INEC ta fitar ya tsara cewa jam’iyyun siyasa na da zuwa ranar 3 ga watan Yuni domin su mika ma hukumar mutanen da suka tsayar a zabukan da ke tafe.”
-
News2 days ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News2 days ago
Zaben 2027: INEC Ta Amince Da Atiku Abubakar, ‘Yan Takarar ADC 470
