Connect with us

News

2023: Ya kamata Shuganbancin kasa ya Koma kudanci a Babban Zaben dake tafe.

Published

on

Daga maryam bashir musa 

 

 

 

Shugabancin majalisar kolin Malaman Addinin Musulumci ta kasa, a ranar Litinin sun bayyana cewa ya kamata Shugabancin kasa a Zaben 2023 dake tafe ya kasance daga kudancin kasa.

Majalisar da take bukatar Shugabanci daga kudanci a Zaben 2023 ba wani yarjejeniyar da aka cimma, a inda Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari zata kawo karshen wa’adinta na shekaru 8 da tayi a Shekara Mai zuwa.

Advertisement

Kungiyar Manyan malaman Addinan musulumcin ta bayyana hakan cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun yada labarai da hudda da jama’ar ta, Sheikh Muhammad Nourayn Ibn-Ahmed, daya fitar a Abuja.

Majalisar ta kuma umarci mabiyanta da kuma Musulmai dasu duba yuwuwar maida Shugabancin yankin kudanci gabannin babban Zaben 2023 domin samar da Adalci, gaskia rukun Amana da daidaito.

Majalisar tace ta la’kari da yadda Shugabanni ke gudanar da mulki a yanzu, maida Shugancin Kudu shine masalaha, Wanda hakan zai samar da inganci wajan zaman lafiya da hadin kan jama’a.

Shugabannin Addinan suna masu cewa sun damu gaya game da kisan da akeyi a kasar da Adduar gaggauta kawo karshen rashin tsaron Da ake fuskanta. Kazalika Majalisar tayi addu’an neman Allah ya amshi ibadunmu da akayi na watan Ramadan duba da yadda duniya ta sauya.

A Karshe cikin Sanarwan, majalisar tayi Addu’ar neman Allah ya kawo karshen lamarin yan bindiga, masu garkuwa da sauran wasu harkokin rashin tsaro a daukacin fadin kasar. Sun kuma bukaci musulmai dasu amfana da darussan da suka koya a watan Ramadan tare da fatan alkairi.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending