Daga Kabiru basiru fulatan
Ministan Shari’a na Najeriya Abubakar Malami ya janye daga takarar gwamnan Kebbi a zaɓen 2023, kamar yadda mai magana da yawunsa ya tabbatar wa BBC.
Umar Gwandu ya kuma ce Malami na nan kan kujerara ta ministan shari’a saɓanin rahotannin da ke cewa ya yi murabus.
Malami wanda ya ayyana aniyarsa ta takarar gwamna a jihar Kebbi ƙarƙashin jam’iyyar APC, ya janye ne bayan shugaba Buhari ya umarci ministocinsa da ke son takara su yi murabus.
