News
MATAN da suke so a daina kyama da tsangwamarsu idan suna jinin haila a fadin duniya
Daga khadija abdullahi mahmud.
Wannan kudirin, wanda aka tattauna a majalisa a ranar Talata 17 ga watan Mayu, na cewa akwai yiwuwar mata za su iya samun hutun kwanaki uku a duk wata idan suna fama da zafin al’ada kuma akwai yiwuwar hutun zai iya kai kwanaki biyar ga wadanda ciwonsu ya yi tsanani.
Sai dai ba a sa ran wannan hutun zai shafi matan da zafin al’adarsu bai da tsanani.
Wannan matakin na daga cikin wani babban kudiri kan batun lafiyar mata da kuma ƴancinsu na haihuwa wanda gamayyar masu ra’ayin gurguzu na ƙasar ke jagoranta.
Idan aka amince da wannan kudiri ya zama doka, zai zama irinsa na faro da aka taɓa samu a duk Turai.
Ƙasashe ƙalilan ne kacal a fadin duniya suka amince a shari’ance da bayar da hutu ga mata masu al’ada -akasarinsu a nahiyar Asia ciki har da Japan da Taiwan da Indonesia da Koriya Ta Kudu da kuma Zambia.
Doka ta farko da aka soma yi kan batun hutu ga masu al’ada ta samo tarihi ne tun a zamanin Tarayyar Soviet inda aka fito da ita a 1922.
Magoya baya sun ce mata na buƙatar irin wannan hutun kamar yadda suke buƙatar hutun haihuwa. Sai dai masu sharhi na nuna cewa irin wannan lamarin zai iya jawo tsangwama da kuma sanyaya gwiwar kamfanoni daga ɗaukar mata aiki.
Shirin BBC na mata 100 rabin muryar al’umma, ya tattauna da wasu mata a wasu ƙasashen da ke da irin waɗannan tsare-tsare na bayar da hutu ga mata masu al’ada domin sanin ko ana samun nasara.
Ma’aikaciyar gidan talabijin ta Indonesia Irine Wardhanie ta bayyana wa BBC cewa tun tana makarantar sakandire take fama da raɗaɗin al’ada. A halin yanu tana ɗaukar hutun kwanaki biyu a duk wata kuma ta buƙaci hakan ne daga wurin aikinta
Irine Wardhanie ta bayyana cewa ko tambayar mata ƙunzugu ana kallonsa a matsayin wani abin ƙi a Indonesia
Irine Wardhanie ta bayyana cewa ko tambayar mata ƙunzugu ana kallonsa a matsayin wani abin ƙi a Indonesi
sannan ta kara da cewa
“Kafin na fara al’ada ina samun ciwo sosai. Ina jin gajiya a tattare da ni kuma ina samun ciwon kai mai tsanani. Idan na fara al’ada, cikina na katsawa sosai. Ina jin amai da kuma zazzaɓi. Wannan na ɗaukar kusan kwana biyu zuwa uku,” .
“Ki yi tunanin zuwa wurin namiji ya buƙaci hutun al’ada.”
“Da farko na damu kan abin da sauran mutane za su rinƙa tunani, sai dai abin ba wahala tamkar tura saƙon e-mail zuwa shugabannina ne kuma suna bani goyon baya,” in ji ta.
“Babu wata wahala a kamfanin da nake aiki, kawai tura e-mail nake zuwa shugabana domin sanar da shi. Shikenan.
“Wasu abokan aikina kaɗan ne kaɗai ke nuna rashin jin daɗinsu sakamakon suna kallon matakin a matsayin rashin adalci.”
Ba kamar Irine ba, mata da dama a Indonesia ba su da masaniya kan wannan doka wadda ke bayar da dama a ɗauki hutun kwana biyu idan suna al’ada.
“Na yi magana da wasu mata da ke aiki a gidajen yaɗa labarai a Indonesia waɗanda ba su da masaniya kan wannan tsari wanda hakan ya tilasta musu su gudanar da ayyuknsu suna cikin zafin al’ada.”
“Matan da ke aiki a irin waɗannan wurare ba su cika sanin batun hutun al’ada ba. Ɗaya daga cikin irin ƙalubalen da irin waɗannan matan ke fuskanta shi ne dole ne su samu takardar shaida daga likita,” in ji Ms Widyawati.
“Sai su fuskanci barazana irin ta cin zarafi ta hanyar lalata ko kuma su ji kunya idan za su nemi irin wannan buƙata. Bugu da ƙari: kamfanoni da dama ba su son biyan kuɗi idan mace na hutun al’ada.”
Mene ne zafin ala’da?
Akasarin mata waɗanda ke al’ada na jin zafi sai dai wasu suna samun zafi mai matuƙar raɗaɗi wanda ke jawowa su kasa kataɓus.
Ana jin zafin ne a mara inda za a ji kamar ciki yana katsawa wanda zafin ke bazuwa har baya zuwa cinya da kuma jin amai da gudawa da cieon kai.
Akwai abubuwa da dama da ke jawo zafin al’ada – misali rashin daidaito a a adadin ƙwayoyin halitta.
Bincike ya nuna cewa zafi da mata ke ji a lokacin al’ada abu ne da ake yawan samu, kuma wannan lamari yana kawo cikas ga yanayin ayyukan mata kusan kaso 20 bisa 100 na matan.
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
