News
Gwamnatin Legas ta ba ƴan kasuwar Alaba Rago wa’adin kwana 14 su tashi
Daga Hamza Yusuf Abdulmumin
Advertisements
Advertisements
Gwamnatin Jihar Legas ta bayar da wa’adin kwana 14 ga duka mazauna kasuwar Alaba Rago su tashi daga kasuwar.
Sarkin kasuwar ta Alaba Rago Alhaji Umar Nagogo Sokoto ya tabbatar wa BBC da ba su wa’adin.
Advertisements
Gwamnatin Legas dai ta bayyana cewa kasuwar ta zama matattarar masu aikata laifuka kuma wannan na daga cikin dalilin da ya sa za a tayar da kasuwar.
Advertisements
Advertisements
Sai dai a cewar sarkin kasuwar, ya musanta wannan zargin inda ya ce hatsaniyar da aka samu inda har aka kama wani da bindiga ƙirar pistol ne ya shafe su kuma ya ce hatsaniyar an yi ta ne a can bayan kasuwar Alaba Rago kuma bai shafe su ba.
Advertisements
