News
Taliban ta umarci ‘yan jaridar talabijin mata su dinga rufe fuskokinsu
Daga Usman Abdullahi jibirin
Gwamnatin Taliban a Afghanistan ta ba wa matan da ke aiki a gidajen talabijin umarnin rufe fuskokinsu a lokacin da suke gabatar da shirye-shirye.
Umarnin zai fara aiki ne nan take ba tare da bata lokaci ba.
Tuni masu fafutika a kasar suka fara nuna rashin jin dadinsu game da umarnin a kafafen sada zumunta.
Akwai sauran matakan da Taliban ta dauka a kan mata da suka hada da tursasa musu rufe dukkan jikinsu idan sun shiga cikin jama’a, da rufe makarantun sakandiren ‘yan mata da kuma hana mata tafiya ba tare da mauharrami ba.
Wani shahararren mai amfani da dandalin Twitter ya ce “wadannan matakai na Taliban wariyar jinsi ce karara”.
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
