Connect with us

News

Soyayyar Ƴan Najeriya Ta Sanya Buhari Yin Fatali Da Kudirin Ƙarin Kudin Kiran Waya

Published

on

Daga Sulaiman ado Ahmed 

 

 

Gwamnatin tarayya ta yi fatali da wani sabon haraji kan kiran wayar tarho a kasar nan domin ba da tallafin kiwon lafiya kyauta ga kungiyar masu rauni a Najeriya.

TA KICIME A APCn KADUNA: Ɓangaren Sha’aban ba su amince da zaben wakilan jam’iyyar APC da aka yi ba

Hakan dai na zuwa ne duk da yunkurin da kamfanonin sadarwa suka yi na kara farashin ayyukansu a sakamakon rashin kyawun yanayi na aikin.

Advertisement

Harajin wayar tarho wanda ya yi daidai da mafi karancin kobo daya a cikin dakika daya na kiran waya wani bangare ne na hanyoyin samun kudaden da ake bukata don samar da su ga bangaren kiwon lafiya kyauta ga Gidauniyar masu rauni a Najeriya.

Wannan yana kunshe ne a cikin kudirin dokar hukumar inshorar lafiya ta kasa 2021 da shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya sanya wa hannu a makon jiya.

Dokar ta hada da wani tanadi da ke karkashin sashe na 26 karamin sashe na 1c wanda ya bayyana cewa tushen kudaden da ake samu na Asusun rukunin masu rauni ya hada da harajin sadarwa, wanda bai gaza kobo daya a cikin dakika daya na kiran waya ba.

Shugaban sashin tattara haraji na bangaren Taiwo Oyedele, ya ce, sashi na 26 na wannan sabuwar dokar da aka sanyawa hannu na cewa harajin sadarwa wanda bai gaza 1kobo ba a dakika daya kan kiran waya shine karin da aka yi.

Tare da farashin kira a kusan kobo 11 a cikin daƙiƙa guda, wannan yana fassara zuwa harajin kashi 9 na kiran waya.

“Harajin yana daya daga cikin hanyoyin samun kudin shiga ga Gidauniyar masu rauni don bayar da tallafin samar da kiwon lafiya ga kungiyar da aka ayyana, wadda ta hada da yara ‘yan kasa da shekaru biyar, mata masu juna biyu, tsofaffi, nakasassu da hankali, da kuma marasa galihu kamar yadda za a iya bayyana daga. lokaci zuwa lokaci.”

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending