Peter Obi na cikin manyan batutuwan da aka fi tattaunawa a Twitter a ranar Talata bayan ya fice daga talakarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP.
Gwamnonin Najeriya za su ɗaukaka ƙara kan ƙayyade kashe kuɗaɗen ƙananan hukumomi
Tsohon gwamnan na Anambra ya fice PDP yana mai bayyana cewa ba zai iya ci gaba da tafiya a jam’iyyar ba.
Ya ce zai ci gaba da bayar da gudunmuwarsa wajen taimakawa Najeriya magance matsalolinta.
Peter Obi ɗan kasuwa ne wanda ya shiga jam’iyyar PDP a 2017.
Ya yi takarar mataimakin shugaban ƙasa tare da Atiku Abubakar a zaɓen 2019.
Babu dai wata manufa da ta fito kawo yanzu kan daliln ficewarsa daga takarar shugaban ƙasa da kuma inda ya dosa.
Amma a kwanakin baya ƴan Najeriya musamman a Twitter sun ta alaƙanta shi da tsohon gwamnan Kano Rabiu Musa Kwankwaso kuma ɗan takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar NNPP.
