Hukumomin Saudiyya sun sanar da sabbin sauye-sauyen da suka tsara na wannan shekarar tare da sanar da duka hukumomin jin dadin na kasashen duniya.
Wadannan dalilan na cikin wadanda suka kara yawan kudaden hajjin da ake ta kokawa da su.
Sakatare hukumar jin dadin alhazai ta Kano Mohammad Abba-Danbatta na cikin wadanda suka halarci wannan taro kuma ya yi wa manema labarai karan bayani
Danbatta ya ce a baya ciyar da alhazai da ake yi a Muzdalifah na hannun hukumomin jin dadin alhazai na kasashe amma yanzu ya dawo karkashin kulawar hukumar alhazai ta Saudiyya karkashin Mu’assasa.
An kara kudin hada wadda kowa ya san zabi ce, wanda hakan ke da alaka da irin hajjin da mutum ke yi, a baya kamar mahajjatan Najeriya na biyan abin da bai fi naira dubu 40 ba, amma a yanzu sai yakai dubu 81.
“Sai biyan harajin kasa da kasa da ko wanne alhaji zai rika yi, wanda shi kuma ya danganta da filin jirgin da mahajjaci ya sauka, na Sarki Abdul’aziz ko na Sarki Fahad, kuma kudin za a biya naira dubu 101,000 zuwa 119,000” in ji Danbatta.
Daga yanzu ko wanne mahajjaci zai rika biyan kudin inshorar lafiya wanda a baya ba a biya kuma kudin sun kai naira 33,000.
Sai harajin kayayyaki da na kama gida da aka kara sanyawa wanda aka kara shi zuwa kashi 15 cikin 100.
Wadannan haraje-haraje sun samu ne sakamakon koma bayan tattalin arziki da ake fama da shi a duniya, wanda matsaloli irin na cutar korona suka janyo.
Wani abu da ya kara yawan kudin ga ‘yan Najeriya shi ne tashin farashin dalar Amurka na duka bangarori biyu, wato farashin gwamnati da na kasuwar bayan fage.
A 2019, an bai wa hukumar jin dadlin alhazai dala a kan naira 306 amma yanzu naira 410 aka ba su, a bayan fage kuwa farashin yakai 600 duk dala daya.
“Wannan ne dalilin da ya sanya a baya muka ce mun sanya naira miliyan 2,500,000 ya zama kudin da za a iya biya na hajji na wannan shekarar, zai iya wucewa ko ya gaza haka”, in ji Danbatta.
