Connect with us

Politics

SABUWAR BARAKA TA KUNNO KAI A APC

Published

on

Daga khadijaAbdullah muhmd

 

Advertisement

 

 

Advertisement

Sabuwar baraka ta kunno kai a tsakanin shugabannin jam’iyyar APC ta kasa inda ake zargin Sanata Adamu da mulki shi kadai

Kamar yadda takardar da mataimakan shugaban jam’iyyar 2 suka fitar, sun bukaci NWC ta hade kai tare da ceto jam’iyyar

Advertisement

A cewar Lukman da Isaac, Adamu na yanke hukunci kuma ya alakanta shi da Buhari ta yadda babu mai iya kalubalantarsa

 

Advertisement

A wata takarda da ta fita a ranar Talata a Abuja, mataimakin shugaban jam’iyyar na kasa na yankin arewa maso yamma, Salihu Mohammed Lukman, da mataimakin jam’iyyar na kasa daga kudu maso yamma, Isaac Kekemeke, sun ja kunnen Adamu kan daukar mataki shi kadai da sunan shugaban kasa Muhammadu Buhari.

 

Advertisement

 

 

Advertisement

Wani sashi na takardar ya bayyana cewa, “A matsayinmu na mambobin NWC da ke da alhakin mambobinmu, muna mika sanarwa ga Abdullahi Adamu, ta kuma hannun shi da ya kira dukkan mambobin APC kan cewa duk wani hukuncin da shugaban jam’iyyar zai yanke ko wani jigo, wanda ke bukatar amincewa kamar yadda kundin tsarin mulkin APC ya bukata, za a dauke shi ba bisa ka’ida ba kuma karantsaye ga dokar NWC, matukar NWC ko wasu daga cikin mambobin kwamitin shugabancin jam’iyyar ba su yarda da shi ba.

 

Advertisement

“Babu mamban NWC da aka zaba a ranar 26 ga watan Maris don ya dumama ofishinsa a sakateriyar jam’iyya ta kasa. A don haka muna kira ga dukkan abokan aikinmu da su tashi tsaye kan wannan kalubalen ta hanyar hada karfi da karfe wurin ceto jam’iyyar mu da dawo da ita zuwa kan turbar da aka gina ta na kawo cigaban Najeriya cike da gaskiya, adalci da kuma jajircewa. Allah ya yi wa jam’iyyar mu albarka!

 

Advertisement

“A cikin watanni biyu kacal na shugabancin da muka yi na jam’iyyar mu karkashin Sanata Abdullahi Adamu, NWC tana da karfin ikon kula da lamurran yau da kullum, har da yanke shawara na NEC kamar yadda sashi na 13, sakin layi na 4 na kundin tsarin

 

Advertisement

“Shugaban jam’iyyar na daukar mataki shi kadai. A lokacin da ya ga dama, yana saka sunan shugaban mu, Shugaban kasa Muhammadu Buhari domin tirsasa mambobin NWC don su yarda da hukuncinsa. Duk wani kokari na ganin cewa shugaban ya mutunta shugabancin NWC kamar yadda aka zabe su a ranar 26 ga watan Maris, ya gagara. A kula cewa, karfin ikon NEC ga NWC ne kuma ba ga shugaban jam’iyyar ko wani ba.

“A matsayin mu na jam’iyya, mun fuskanci tozarci na shari’a da ke tasowa daga take dokar kundin tsarin jam’iyya. Ya zame mana dole mu fitar da wannan sanarwar ne saboda jerin yadda ake ta dage taron NWC, har sau biyu cikin sa’o’i 48.”

Advertisement

 

 

Advertisement

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending