Connect with us

Politics

‘Yan Najeriya na kewar shekaru 16 na mulkin PDP – Babangida Aliyu.

Published

on

Daga khadija abdullahi muhmd 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

Dan takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar PDP Atiku Abubakar ya ce ya daura damarar fara yakin neman zabe domin tabbatar da karbe ragamar Najeriya a 2023.

 

Advertisement

Dan takarar ya bayyana haka ne a lokacin da jam’iyyar PDP ta mika wa Alhaji Atiku Abubakar shaidar zama dan takarar ta a zabe mai zuwa.

 

Advertisement

BBC ta tattauna da Dr. Mu’azu Babangida Aliyu shugaban tsofaffin gwamnonin jam’iyyar ta PDP, kan shirinsu na tunkarar zaben badi.

 

Advertisement

“Na daya mu a jam’iyyarmu, mun tsayar cewa shugaban jam’iyyar zai fito ne daga kudu. Sai wani wanda ke ganin yana da wayo ya sa muka dawo da mukamin arewa, inda matakin ya sa muka bar kowane dan Najeriya ya nemi takara, muka kuma yi shi a rubuce. To kaga tsarin karba-karba an yi shi ne domin a sa harsashin gina dimokradiyya. Amma bayan wani lokaci, sai a bari duk wani mai kwazo ya fito.”

 

Advertisement

BBC: Amma ba ku da farga cewa APC na iya muku bita da kulli a lokacin zabe mai zuwa?

 

Advertisement

Babangida Aliyu: “A’a, wannan kuma na Allah ne. Kuma duk abin da za su yi ba zai hana mu samin kuri’u daga can ba.”

 

Advertisement

BBC: Kaman kuna sane da shirin da jam’iyya mai mulki ke yi na ci gaba da rike mukamin shugaban Najeriya?

 

Advertisement

Babangida Aliyu: “Wallahi ba komai. Ba Allah ne ya kawo su ba? Ai da Alah ya tashi kawo su, da mu yayi amfani, ya sa wasunmu suka koma jam’iyyarsu. Kar ka manta cewa gwamnoni biyar suka fita daga PDP suka koma jam’iyyarsu. Da wadannan gwamnonin biyar ba su fita ba, da babu inda za su kai.”

 

Advertisement

BBC: Shin wadanne abubuwa kuke son sa wa a gaba idan kuka sami damar komawa bisa karagar mulki?

 

Advertisement

Babangida Aliyu: “Dan takararmu ya ce akwai abu biyar da yace zai mayar da hankali akai. Cikinsu, na daya shi ne hadin kai, na biyu tabbatar da tsaro domin da ma babban aikin gwmanati ke nan, cewa ta tsare rayuka da dukiyoyin al’umarta.”

 

Advertisement

Ya kuma kara da cewa, “Allah ya taimake mu. ‘Yan shekaru 16 nan da muka yi kan mulki sun shiga zukatan ‘yan Najeriya har ta kai ga suna kewar mu saboda tabarbarewar da abubuwa suka yi a yanzu.”

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending