News
Koriya ta Arewa zata sake gwada makamin nukliya
Daga Sulaiman ado Ahmed
Hukumar kula da makamashin Nukiliya ta MDD ta ce Koriya ta Arewa na shirin gudanar da wani gwajin makamin nukiliya.
Koriyan dai ta taba gudanar da gwajin makamin a 2017.
Shugaban hukumar makamashin Rafael Grossi,ya ce akwai alamomi da ke nuna an buɗe cibiyar da ake gwajin.
A shekaru huɗu da suka gabata Koriya ta Arewa ta ce ta rufe cibiyar, wato wurin da take gwajin nukiliya.
Mista Grossi, ya ce fashewar za ta ci karo da kudurorin kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya,kuma zai haifar da ‘ babbar damuwa’.
A tsawon makwanni ana ta fargabar cewa Pyongyang na shirin gudanar da wani gwajin makamin nukiliya.
Advertisements
