Connect with us

News

Shekara guda kenan da garkuwa da ‘yan mata ɗalibai a Yawuri

Published

on

Daga Muhammad Muhammad zahraddin

A wannan Juma’ar ake cika shekara ɗaya da sace gomman ɗaliban Kwalejin Tarayya ta Yauri.

Iyaye na ci gaba da kwanan takaici da baƙin cikin rayuwa saboda rashin kuɓutar da ragowar ‘ya’yansu.

Tun bayan sace ɗaliban a ranar 17 ga watan Yunin bara, hukumomi sun yi ƙoƙarin kuɓutar da wasu daga cikin ɗaliban lokaci zuwa lokaci.

‘Yan fashin daji dai sun ci gaba da tsare ɗalibai ‘yan mata 11, waɗanda wasu rahotanni suka riƙa cewa an aurar da su.

A ranar 16 ga watan Yunin shekarar 2021 ne ‘yan bindigar suka sace wadannan dalibai sama da 100 daga makarantarsu da kuma wasu malamai suka nausa daji da su.

Advertisement

A saurari rahoton Imam Saleh domin samun wasu bayanai kan yanayin da ake ciki game da daliban da ke hannun ‘yan bindiga.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending