Daga Kabiru basiru fulatan
Hukumar hana fasa-kwauri ta Najeriya ta sanar da manema labarai cewa ma’aikatanta sun kama kayan da aka yi sumogal dinsu, kuma masu kayan sun biya Naira miliyan 38 cikin wannan watan da ake ciki.
Babban jami’in da ke kula da ofishin hukumar a Jihar Katsina, Dalhatu Chidi-Wada ne ya sanar da haka yayin wata ganawa da yayi da manema labarai a Katsina.
Jaridar Punch ta ruwaito cewa bude kan iyakar Najeriy ada Nijar a garin Jibia ya taimaka wa yawancin al’umomin yankin su gudanar da harkokin kasuwancinsu kamar yadda doka ta tanadar.
Dalhatu Chidi-Wada ya ce yawan kayan da ake shigarwa da fitarwa kan iyakar ta Jibia cikin watan da ya gabata ya hada da tan 4,000 na nau’in gas na LNG da tan 1,000 na siminti.
