News
Mun kori malamai 2,357 ne saboda basu cancanta ba” Gwamnatin jihar Kaduna.
Daga kabiru basiru fulatan
Gwamnatin jihar kaduna ta bayyana cewa takori malamai 2,357 ne saboda saboda basu cancanta ba kuma sun fadi a jarabawar databyi masu.
Babu kasar da tafi Najeriya yawan yara maras zuwa makaranta, Bankin Duniya
Alhahi Tijjani Abdullahi Shugaban kungiyar ilimin na Kaduna, kuma suruki ga Gov Nasuru El-Rufai yace a shekarar 2021 gwammatin jihar ta yiwa malamai 30,000 jarabawa.
Inda yace an kori malamai 2,192 na firamari hadda shugaban kungiyarsu ta NUT, Audu Amba saboda sunki zuwa rubuta jarabar.
Yayin da kuma aka kori 165 cikin 27,662 da suka rubuta jarabawar saboda basu cancanta ba.
Advertisements
