News
Jam’iyyar NNPP Tayi Allah-Wadai Da Korar Malaman Makaranta Sama Da Dubu Biyu A Jihar Kaduna
Daga Khadija Abdullahi Mahmud
Jam’iyyar NNPP ta bayyana damuwarta kan korar malamai sama da 2,000 da aka yi a jihar Kaduna saboda gazawar da suka yi a jarrabawar tantancewa, yayin da ta dora wa Gwamna Nasir El-Rufai aikin shirya horarwa a maimakon tura su kasuwa mai cike da ma’aikata.
Mun kori malamai 2,357 ne saboda basu cancanta ba” Gwamnatin jihar Kaduna.
A cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun dan takararta na gwamna a jihar Kaduna, Sanata Suleiman Hunkuyi a ranar Talata, NNPP ta ce kamata ya yi gwamnatin jihar Kaduna ta samar da ayyukan yi ga al’ummar jihar maimakon korar wadanda suka rigaya suka dauka aiki.
“Jam’iyyar NNPP da dan takararta na gwamna, Sanata Suleiman Othman Hunkuyi sun yi nuni da cewa, sun yi matukar kakkausar suka ga tsarin kyamar jama’a da Gwamna Ahmed Nasir El-Rufa’i na jam’iyyar APC yake jagoranta na ci gaba da korar malaman makarantun firamare a jihar a karkashin tsarin jarabawar cancanta da ba a gama ba. .
“Jam’iyyar NNPP da dan takararta na gwamna suna tunatar da gwamnatin El-Rufa’i cewa babban nauyi ne da ya rataya a wuyan gwamnati na samar da ayyukan yi ga ‘yan kasa, ta yadda za su inganta rayuwarsu.
“Tun daga lokacin da aka kafa gwamnatin APC, an ba da fifikon da bai kamata ba, ga yadda ake tafka ta’asa da ta’addanci da ake yi wa ma’aikata, musamman wadanda ke cikin bangaren ilimi (malaman makarantun firamare) a karkashin rugujewar rashin kwarewa.
“Jam’iyyar NNPP na kallon korar malamai 2,357 na baya-bayan nan tare da matukar damuwa. Wani abin kyama shi ne idan bayan shekara bakwai gwamnatin El-Rufa’i ta kasa samar da kwararrun malamai a makarantun firamare a jihar, babu abin da ya fi tada hankali.
“Jam’iyyar NNPP tana tunatar da gwamnatin El-Rufa’i cewa duk wadannan ma’aikatan da aka kora ba za a ce ba su da aikin yi. Bugu da ƙari, alhakin gwamnati ne don tabbatar da ci gaban ma’aikatanta a matakin farko.
“Saboda haka, muna jajantawa tsohon shugaban kungiyar NUT na kasa, Mista Amba Audu, da kuma duk sauran korarrun malamai da ma’aikatan gwamnati. Muna rokon su da su ci gaba da kwantar da hankula, muna kuma ba su tabbacin cewa za a sake duba wannan babban rashin adalci a kan lokaci,” in ji Sen. Hunkuyi.
-
Opinion7 days ago
Ayyuka, Bin Diddigi, Biyan Kudi, Sakamako: Dabarun Kano Da Suka Zarce Jihohi 35
-
Opinion7 days ago
Tiriliyan ₦210 na Karya: Yadda Bala Wunti Ya Warware Dukkan Rudanin da Ya Mamaye Zaman Majalisar Dattawa Kan Asusun NNPC
-
News5 days ago
Likitan El-Rufai Ya Shiga Matsala Kan Zargin Bayar Da Rahoton Jinya Na Bogi
