News
Gasar Firimiya ta Ƙasa: Ciyaman ɗin Pillars ya naushi mataimakin alƙalin wasa a Kano
Daga Yasir sani abdullahi
Ciyaman ɗin ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Kano Pillars, Shu’aibu Yahaya Jambul ya naushi mataimakin alƙalin wasa a wasan da kungiyar ta doke ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Dakkada 1-0 a filin wasa na Sani Abacha da ke Jihar Kano.
Babu Sauran Gurbi Ga Mahajjatan Najeriya Na Bana – NAHCON
Daily Nigerian Hausa ta rawaito cewa tun a minti na 22 na wasan ne dai ɗan wasan gaban Pillars, Yusuf Maigoro ya jefa ƙwallo ɗaya tilo a ragar Dakkada.
A na tsaka da wasan ne dai a daidai lokacin tashi sai Dakkada ta farke kwallon, lamarin da ya fusata Jambul, har ta kai ga ya naushi mataimakin alƙalin wasa, wanda shine ya amince da cewa kwallon ta ci.
Bayan da ƴan wasan Pillars sun yi bore a kan ƙwallon, sai alƙalin wasa, bayan ya tattauna da sauran nataimakansa, sai ya gane cewa an yi satar gida wajen cin ƙwallon, sabo da haka sai ya soke ta.
Wannan harin da Jambul ya kaiwa mataimakin alƙalin wasa ne ya sanya a ka tashi a wasan, inda ƴan sanda ɗauke da makamai su ka raka ƴan wasan Dakkada ɗin zuwa masaukinsu da ke unguwar Sabongari.
Daily Nigerian Hausa ta rawaito cewa yanzu dai a na jiran a ga ko wanne irin hukunci hukumar Gasar Firimiya ta ƙasa za ta yanke a kan ciyaman ɗin da ma kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars.
-
News1 day ago
Jam’iyyar Labour Party Ta Yi Alkawarin Kafa Hukumar Kula Da Hayar Gidaje A Kano
-
News3 days ago
Shettima @60: Haƙurinsa, Biyayyarsa Sun Taimaka Wajen Ciyar Da Manufofin Shugaba Tinubu Gaba — Kwankwaso
-
News6 days ago
KANO:’Yan Mata Uku ’Yan Gida Ɗaya Sun Mutu A Kifewar kwale-kwale A Tiga
