Connect with us

News

Babu Sauran Gurbi Ga Mahajjatan Najeriya Na Bana – NAHCON

Published

on

Daga Usman Abdullahi jibirin

 

Advertisement

 

 

Advertisement

Hukumar Alhazai ta Najeriya NAHCON, ta ce tana son sanar da Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihohi, Ma’aikatu/Hukumomi, Masu Shawarwari da bayar da Lasisi, da sauran al’umma cewa kason Alhazan da aka ware wa Najeriya gaba daya ya kare tun kafin yanzu.

Mazauna Kano sun Koka kan rushe Azuzuwa domin gina Shaguna

Advertisement

A cikin wata sanarwa da Fatima Sanda Usara, AD, mai kula da harkokin jama’a ta sanya wa hannu, hukumar ta ce tana fatan daukacin manajojin aikin Hajji sun yi amfani da kason su bisa la’akari da yadda aka fara gudanar da aikin kamar yadda aka amince tun fara gudanar da ayyukan.

 

Advertisement

 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

 

Sai dai kuma ta ba da tabbacin cewa, idan Saudiyya ta mutunta bukatar ta na neman karin mukamai, hukumar za ta raba wa duk masu ruwa da tsaki da ke neman karin kaso ba tare da bata lokaci ba.

Advertisement

 

A halin da ake ciki, NAHCON ta bukaci daukacin hukumomin alhazai na Jihohi da masu zaman kansu da su kara mayar da hankali wajen shirya mahajjatansu domin isar da su zuwa kasar Saudiyya kan lokaci.

Advertisement

 

 

Advertisement

 

Ta ce bukatar a kwashe dukkan maniyyatan da suka yi rajista zuwa kasa mai tsarki lafiya kafin rufe sararin samaniyar Saudiyya shi ne abin da ya fi daukar hankalin NAHCON a halin yanzu.

Advertisement

 

Kazalika, hukumar ta tabbatar wa masu gudanar da balaguron da bayar da lasisin cewa an samu nasarar shawo kan kura-kuran da aka samu a farkon sabon tsarin aiki, inda ta kara da cewa ana sa ran za su fara buga takardun balaguronsu ba tare da bata lokaci ba.

Advertisement

 

 

Advertisement

 

Haka kuma, an shawarci maniyyatan da suka yi rajista da su bi umarnin manajojin su, domin kammala aikin Hajjin bana na 2022 ba tare da tangarda ba.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending