Connect with us

News

Hukumar Hisbah Za Ta Kafa Sharruda Kan Kafofin Sada Zumunta.

Published

on

 

Daga Muhammad Muhammad zahraddin

 

 

Hukumar Hisbah ta Jihar Kano tana shirin yin dokar kafa sharruda kan amfani da kafafen sada zumunta wato soshiyal midiya. Domin hakan, hukumar tana hadin gwiwa ne tare da Hukumar Tace Fina-Finai Ta Kano (KSCB).

Babban Direktan KSCB, Ismail Na’abba Afakallah, ne ya bayyana hakan yayin wata hira da aka yi da shi.

Advertisement

Ya ce hukumar ta sa za ta mayar da hankali ne sosai kan fim industry, soshiyal midiya, musamman TikTok, da ya bawa masu karfin fada a ji a dandalin sada zumunta aikata badala.

“Hukumar mu da Hisbah ta kafa kwamiti da zai samar da hanyoyin magance wannan matsalar.

Ba jaruman Kannywood kadai ke aikata badala ba a Tik Tok, mafi yawancin masu badala da shi ba yan industry bane. “Kallubale ne da ya shafi duniya.

Mutane na ganinsa cewa duniya ce kuma za su iya duk abin da suke so. Kuma ba za mu iya barin hakan ya bata tarbiyar yaran mu ba.

Mun damu da yan Tik Tok wadanda ba yan fim bane saboda suna bata tarbiyyar yaranmu.

Ba za mu amince da rashin tarbiyya ba. Dandalin ya zama sanadin kashe aure, bata tarbiyya da wasu abubuwan.”

Advertisement

Afakallah Ya bayyana damuwarsa kan cewa an kirkiri dandalin sada zumunta ne don nishadi da watsa bayanai masu amfani amma mutane suna amfani da shi ta hanyar da bai dace ba.

Yace “Yanzu suna amfani da damar don yada bayanai marasa amfani. Za ka ga manyan mata suna tika rawa na rashin mutunci da wasu abubuwan rashin tarbiya, musamman a Tik Tok da Instagram.”

Ya yi kira ga iyaye su saka idanu kan abin da yayansu ke yi a soshiyal midiya don kada su lalace.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending