Connect with us

News

Yan bindiga Sun Sace DPO a Jihar Nasarawa

Published

on

Daga Hamza Yusuf Abdulmumin

 

Rahotanni daga jihar Nasarawa na cewa an yi garkuwa da shugaban jami’an yan sanda na karamar hukumar Nasarawa-Eggon.

Rahotannin sun ce CSP Haruna AbdulMalik na sintiri ne a ranar Laraba da daddare tsakanin Eggon-Akwanga, a lokacin da yan bindiga suka fara harbi ba-ji-ba-gani, kafin su yi awon gaba da shi.

Wata majiya ta ce DPO ya samu labarin cewa ‘yan bindiga na hari a karamar hukumar Nasarawa Eggon, kuma yayin da yake kokarin kai dauki ne yan bindigar suka sace shi.

Al’ummar yankin sun bayyana CSP Haruna AbdulMalik a matsayin jajirtaccen dan sanda, da ke taka rawa wurin tabbatar da tsaro a Nasarawa-Eggon.

Advertisement

A jihar Bauchi kuma Rundunar ‘yan sanda ta jihar ta tabbatar da tsintar wani yaro da aka kwakule wa idanu, a anguwar Dutsen Jira da ke garin Bauchi.

Wata sanarwa da rundunar ta fitar ranar Juma’a ta ce da misalin karfe shida na yamman ranar Alhamis ne aka ankarar da jami’na tsaron cewa na tsinci Uzairu Salisu, mai shekaru 16, kwance cikin jini wasu da kawo yanzu ba a san ko su waye ba, suka kwakwale mashi ido.

A cewar matashin wani mutum da ya kira Ibrahim Rafin Zurfi ne ya neme shi da ya zo ya mishi aiki a gonar shi, to amma bayan sun isa sai ya shake shi da waya, ya kuma kwakwale masa ido.

Yanzu haka rundunar ta ce matashin na jinya a asibitin koyarwa na Tafawa Balewa da ke Bauchi.

Kwamishinan ‘yan sanda a jihar Bauchi CP Umar Mamman Sanda ya ce suna gudanar da bincike kan batun.

Ya sha alwashin kamawa da hukunta mutanen da suka yi wannan mummunar aika-aika.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending