Connect with us

News

Karancin Na’urorin Tace Jini Yana Barazana ga Rayukan Masu Ciwon Koda a Kano. 

Published

on

Daga kabiru basiru fulatan 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

Rahotanni na cigaba da tabbatar da yadda harkar kiwon lafiya a jihar Kano ke tsaka mai wuya, bayan cigaba da samun masu fama da cutar koda a jihar nan.

Tsananin Yunwa, Hawan Jini Da Damuwa Sun Hallaka Yan gudun Hijira 23 A Katsina

Advertisement

Kamar yadda jaridar PRNigeria ta fitar da rahoto a ranar Lahadi 26 ga watan Yuni, an gano yadda matsanancin ciwon koda (CKD) ke cigaba da kamari a Kano.

 

Advertisement

Wani rahoto yayi nuni da yadda a kalla masu fama da cutar koda 200 ke dogaro da injina 12 na tace jini a manyan asibitoci biyu a Kano, wato asibitin koyarwa na Aminu Kano (AKTH) da asibitin kwararru na Abdullahi Wase.

 

Advertisement

Bincike ya tabbatar da yadda kimanin marasa lafiya 160 da ke fama da cutukan da suka shafi koda ke ziyartar asibitin kwararru na Abdullahi Wase duk karshen mako.

 

Advertisement

Haka zalika, akwai a kalla marasa lafiya 15 da ke zuwa gwajin cutar a asibitin kwararrun duk karshen mako.

 

Advertisement

Yayin da asibitin koyarwa na Aminu Kano ke tarbar marasa lafiya 70 duk karshen mako don tace jini sakamakon cutar ta koda.

 

Advertisement

Sai dai a mako guda ake kula da a kalla marasa lafiya 40 ko fiye yayin da saura ke zaman jira.

 

Advertisement

Binciken ya gano da yawan sauran injinan tace jinin na masu cutar kodar a manyan cibiyoyin magance cutar a Kano basa aiki.

 

Advertisement

Har ila yau, an gano yadda a asibitin koyarwa na Aminu Kano, takwas ne kacal daga cikin injinan ke aiki a yanzu, marasa lafiyar da ke fama da cutar koda na daukar tsawon awa 10 suna jira kafin layi yazo kansu.

 

Advertisement

Yayin martani ga lamarin, Farfesa Aliyu Abdu, wanda babban likitan koda ne kuma shugaban sashin kula da koda a asibitin koyarwa na Aminu Kano, ya ce yana da matukar wahala iya aiki da tsirarun injinan tace jini tare da marasa lafiya masu dumbin yawa suna jira.

 

Advertisement

A cewarsa: “A da muna da injinan tace jini na masu cutar koda guda 20, amma saboda karancin hannun jari a harkar lafiya a yanzu bama da fiye da injina biyar lafiyayyu. “Yana da matukar wahala jure hakan.

 

Advertisement

Za ka ga marasa lafiya na zaman jiran wajan awanni 10 zuwa 15 don a lura da matsalar kodarsu saboda idan ka dora mara lafiya kan Injin kula da cutar, dole mara lafiyan ya dauki tsawon awanni 4 a ciki, sannan kana bukatar wata awa daya don gyara gami da kashe kwayoyin cutar injin din kafin wani mara lafiyan ya samu damar shiga.”

 

Advertisement

Saboda haka, idan za ka gani a rana, ba za ka iya daukar fiye da marasa lafiya uku ba a inji daya.”

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending