Connect with us

Sports

Ganduje ya naɗa sabon Ciyaman ɗin Kano Pillars 

Published

on

Daga Maryam bashir musa 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

A yau Laraba ne dai Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya maye gurbin Ciyaman ɗin Kungiyar Ƙwallon ƙafa ta Kano Pillars, Surajo Shuaibu Yahaya, da shugaban Hukumar Wasanni ta Jihar Kano, Ibrahim Galadima.

.Hajjin bana: Ɗaya daga cikin alhazan Jihar Nassarawa ta rasu a Makka

Advertisement

Jaridar indaranka ta rawaito cewa a ranar Asabar ne Hukumar Shirya Gasar Firimiya ta Ƙasa, LMC ta kori tsohon Ciyaman ɗin na Kano Pillars, Suraj Yahaya, wanda a ka fi sani da Jambul daga ƙungiyar.

 

Advertisement

LMC ta ce korar Ciyaman ɗin ta biyo bayan laifin cin zarafin mataimakin alƙalin wasa.

 

Advertisement

A wata sanarwa da ya fitar ta hannun babban sakataren yaɗa labaransa, Abba Anwar, Ganduje ya ce “Kamar yadda kungiyar Kano Pillars ke kara fuskantar matsin lamba a gasar firimiya ta kasa, zai yi kyau a samu shugabancin da zai jagoranci ƙungiyar.”

 

Advertisement

“Ibrahim Galadima, shugaban hukumar wasanni ta jihar Kano, yanzu zai maye gurbin Ciyaman ɗin Kano Pillars FC na yanzu, Surajo Shu’aibu Yahaya, a matsayin muƙaddashi, kafin a naɗa Ciyaman na dindindin,” Gwamna Ganduje ya bayyana a cikin sanarwar.

 

Advertisement

Sanarwar ta ce nadin na nan take ne.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending