News
Rundunar sojin Najeriya ta musanta cewa sojoji za su yi zanga-zanga a Abuja
Daga mujahid danlami garba
Rundunar sojin Najeriya ta ce wadanda suka kirkiri labarin ba za su nasara baImage caption: Rundunar sojin Najeriya ta ce wadanda suka kirkiri labarin ba za su nasara ba
YADDA KA HALAKA WANI MUTUMIN DA YA GOYI BAYAN BATANCI GA ANNABI
Rundunar sojin kasa ta Najeriy ta karyata rahotannin da ake ydawa ta shafukan intanet cewa sojoji na shirin tattaruwa a Abuja domin gudanar da zanga-zanga kan kin biyansu albashi da rashin kyawun yanayin aikinsu da sauran korafe-korafe.
A martanin da ta mayar mai dauke da sa hannun darektanta na hulda da jama’a Birgediya Janar Onyema Nwachukwu a jiya Laraba, rundunar ta ce, sanarwar wadda ake yadawa a shafukan sada zumunta da muhawara wadda ba ta dauke da sunan wani ko wata, ba aba ce da za ta damu da ita ba.
Amma ganin irin girman zarge-zargen da ke cikinta da kuma mummunar manufar wadanda suka kirkiri labarin ya sa ta yi martani.
Rundunar ta ce babu wani lokaci da ta taba mayar da hankali wajen tabbatar da kyautatuwar yanayin aikin sojoji da samar da kayan aiki, kamar a yanzu karkashin shugabancin babban hafsanta Laftana Janar Faruk Yahaya, abin da ya sa sojoji suka kasance da kwarin guiwa wurin gudanar da ayyukansu a yanzu.
Sanarwar ta ce bayan biyan albashi da alawus-alawus na sojojin da kula da lafiyar wadanda aka jikkata da kuma bai wa wadanda ke fagen daga damar zuwa su gana da iyalansu, a yanzu ana bai wa ‘ya’yan wadanda aka kashe a bakin aiki tallafin karatu.
Rundunar ta ce aniyar masu yada wannan labari na shirin zanga-zanga it ace haifar da rabuwar kai tsakanin sojojin Najeriya ta bangaren kabilanci da addini, wanda kuma ta ce ba za su yi nasara ba, saboda kan rundunar a hade yake ba tare da wani bambanci ba.
