Connect with us

News

YADDA KA HALAKA WANI MUTUMIN DA YA GOYI BAYAN BATANCI GA ANNABI

Published

on

Daga Abdullahi Mahmud.

 

Advertisement

 

 

Advertisement

Wani mutum ‘dan yankin Hindu mai sana’ar tela a Indiya ya rasa ransa bisa zarginsa da goyon bayan batanci ga Annabi Muhammad SAW wanda wani yayi

Kanhaiya Lal ya dora wata wallafa a shafinsa yanar gizo inda ya marawa maganar wani kakakin jam’iyyar BJP da ya yi na batanci ga Annabi Muhammad, a baya

Advertisement

Bayan da ake zargi da halakasa sun zo masa shagon dinkinsa ne a matsayin kwastomomi, daga bisani suka aikasa barzahu yayin da ya yi kokarin gwadasu kafin ya dinka musu kaya

An yi bidiyon wanda lamarin ya auku dashi yayin da aka halaka shi tare dorawa a yanar gizo.

Advertisement

Kamar yadda BBC ta ruwaito, makasansa sun yi ikirarin cewa sun yi hakan ne don daukar fansa a kan mutumin bisa marawa maganar Nupur Sharma, wanda kakakin jam’iyyar Bharatiya Janata ta kasa ne (BJP), wacce ta janyo cece-kuce a kan Annabi Muhammad.

 

Advertisement

An gano yadda Sharma ya yi furucin, wanda ake gani a matsayin laifi kan Annabi Muhammad yayin wata muhawara a watan Mayu.

 

Advertisement

An zargi Lal da yin wata wallafa a shafin sada zumuntar zamani tare marawa furucin Sharma.

 

Advertisement

Foreign Newspaper ta bayyana yadda aka gano biyun da ake zargi a bidiyon gami da kamasu.

 

Advertisement

Haka zalika, gwamnatin Indiya ta dakatar da amfani da yanar gizo na wani lokaci tare da haramta dandazon taro.

 

Advertisement

Maganar da ‘dan siyasan ya yi ta janyo zanga-zanga a wasu jihohin kasar, tare da janyo rikici da kasashen musulmai da dama wadanda suka hada da UAE, Iraq da Libya, inda suka yi Allah wadai da furucin Sharma.

Manyan ‘yan siyasa sun yi Allah wadai da halaka mutumin a Indiya.

Advertisement

Haka zalika, wasu fitattun kungiyoyin musulunci sun nuna rashin jin dadinsu kan kisan.

 

Advertisement

“Daukar doka a hannun mutum gami da halaka mutum ta hanyar ayyanashi a matsayin mai laifi ba dabi’a mai kyau bace. Doka bata amince da haka ba kuma shari’ar musulunci bata amince ba,” kamar yadda kungiyar shari’ar musuluncin Indiya ta bayyana a wata takarda.

A Najeriya, Deborah Samuel, wata daliba a Kwalejin ilimi na Shehu Shagari ta rasa ranta bisa furucin da tayi a watan Mayu wanda batanci ne ga Annabi Muhammad.

Advertisement

 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending