Connect with us

News

MASU ZANGA ZANGA SUN MUTU A SUDAN

Published

on

Daga Khadija Abdullahi Mahmud.

 

Advertisement

 

 

Advertisement

Masu zanga-zanga tara sun gamu da ajalinsu sakamakon aranagamar da ta barke tsakaninsu da jami’an tsaro a wasu sassan Sudan ciki har da babban birnin kasar Khartum.

 

Advertisement

Dubun-dubatar ‘yan kasar Sudan sun fito yin tattaki a wannan Alhamis a cigaba da nuna adawa da gwamnatin mulkin soja karkashin jagorancin Janar Abdel Fattah al-Burhane, sai dai daga bisani zanga-zangar ta rikide inda ta koma batakashi tsakanin jami’an tsaro da masu rajin kare dimukuradiyya.

Za a fara zanga-zangar tabbatar da mulkin dimokuradiyya a Sudan

Advertisement

Masu fada a ji daga sassan duniya suka fara sukan lamirin amfani da karfin tuwo wajen tarwatsa masu bore a Sudan, tare da kira ga bangarorin da ba sa jituwa da su saka wa zukatansu ruwan sanyi.

 

Advertisement

Boren kin jinin gwamnatin mulkin soja ya karade kasar Sudan ne tun bayan da Janar Abdel Fattah al-Burhane ya karbe iko da tsinin bindiga daga wata gwamnatin farar hula ta wucin gadi watanni takwas da suka gabata.

 

Advertisement

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending