Haduran mota da aka samu a sassan Najeriya daban-daban a karshen makon sun yi sanadiyyar mutuwar motum 30 tare da raunata wasu da kuma asarar dukiya.
Ma’aikatar lafiya ta tabbatar da ɓullar Kwalara a Kano
Hukumomin kasar sun danganta haduran da saba ka’idojin hanya da gudun da ya wuce kima da kuma tafiye-tafiyen dare.
Jaridar DailyTrust ta kasar ta ruwaito cewa daga cikin haduran, wasu da suka auku a tsakanin ranakun Asabar da Lahadi, sun yi sanadiyyar mutuwar mutum 18 a gadar Isara da ke jihar Ogun, kan tagwayen hanyar Lagos zuwa Badun.
Sannan wasu mutum 10 sun rasu a kan titin Potiskum zuwa Gombe a Jihar Yobe, yayin da wasu mutum biyu suka rasu a wani hadarin motar a kan titin Lokoja zuwa Obajana zuwa Kabba.
A hadari na hudu, wanda shi kuwa ya rutsa ne da kwambar motocin Gwamnan Jihar Benue, Samuel Ortom, a Abuja, rahotanni sun ce motoci hudu wasu tireloli biyu suka murkushe, yayin da wata motar jami’na tsaro a kwambar ta yi karo da wata motar kirar Golf, sai dai ba wanda ya rasa ransa, a hadarin.
