Shugaban Sojin Sudan Janar Abdel Fattah al-Burhan ya ce sojoji za su janye su bada dama ga gwamnatin farar hula.
A jawabinsa a kafar talabijin, ya ce sojoji ba su shiga sha’anin mika mulki ga farar hula ba, kuma a shirye suke su tabbatar da an yi zaɓe.
Jama’a a Sudan na ci gaba da zaman ɗar-ɗar
Masu rajin tabbatar da dimokuradiyya sun shafe kwanaki suna zanga-zanga a sassan Sudan inda suke neman kawo ƙarshen mulkin soji.
A baya, Janar Burhan ya yi watsi da kudirin miƙa mulki ga farar hula.
Tun da farko hukumomi sun saki masu fafutika ɗari da arba’in waɗanda aka kama lokacin zanga-zanga a ranar 30 ga watan Yuni.
Sama da mutum 100 aka kashe tun bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a watan Oktoba.
