Connect with us

News

Uba Sani ya zaɓi Hadiza Balarabe a matsayin mataimakiya a takarar gwamnan Kaduna

Published

on

 

Daga Khadija Abdullahi Mahmud

 

 

 

Ɗan takarar gwamnan Kaduna a ƙarƙashin Jam’iyyar APC Sanata Uba Sani ya ɗauki mataimakiyar gwamnan Kaduna ta yanzu wato Hadiza Sabuwa Balarabe a matsayin mataimakiya a takarar zaɓen 2023.

Advertisement

 

Sanata Sani ne ya bayyana haka a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook inda ya ce ya yi wannan zaɓe ne bayan ya tuntuɓi masu ruwa da tsaki na Jihar Kaduna.

Girgizar kasa ta hallaka mutum 42 a India

Sanata Uba Sani ya bayyana cewa Hadiza ta bayar da muhimmiyar gudunmawa a gwamnatin Malam Nasir El-Rufai wajen gudanar da ayyukan ababen more rayuwa da kuma gina rayuwar al’umma.

 

Sanata Uba Sani na Jam’iyyar APC zai kara ne da Isah Ashiru Kudan na Jam’iyyar PDP a zaɓen 2023 da ke tafe.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending