Connect with us

News

Al’ummar Jihar Osun sun zaɓi wanda suke so – Buhari

Published

on

Muhammad Buhari

Daga yasir sani Abdullah 

 

 

 

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya taya Sanata Ademola Adeleke na Jam’iyyar PDP murnar lashe zaɓen Jihar Osun da aka gudanar a ranar Asabar.

 

Advertisement

Shugaban ya bayyana haka ne a wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Facebook inda shugaban ya ce jama’ar Jihar Osun sun nuna ra’ayinsu ta hanyar jefa ƙuri’a inda ya ce dole ne a girmama abin da mutane suke so a dimokraɗiyya.

Mutumin Da Ya Auri Jikarsa A Zamfara Ya Ki Rabuwa Da Ita

Shugaban ya bayyana cewa gudanar da zaɓen da aka yi lafiya wata alama ce da ke nuna cewa an samu ci gaba da kuma haɗin kan masu ruwa da tsaki da kuma hukumar zaɓe da jami’an tsaro da jam’iyyu da yan jarida da ƙungiyoyi masu zaman kansu da masu zaɓe domin ƙara inganta harkar zabe a Najeriya.

 

Shugaban ya kuma ƙara jaddada aniyarsa ta gudanar da ingantaccen zaɓe a lokacin mulkinsa.

 

Advertisement

 

 

 

 

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending