Sports
Zlatan ya ƙara kwantaragin kaka ɗaya a AC Milan
Daga yasir sani Abdullah
Zlatan Ibrahimovic ya saka hannu kan ƙarin kwantiragin kaka ɗaya, domin ci gaba da taka leda a AC Milan.
Ɗan kwallon tawagar Sweden, wanda zai cika shekara 41 da haihuwa cikin watan Oktoba, ya ci kwallo takwas a bara a kakar da Milan ta lashe gasar Serie A ta ƙasar Italiya.
Gwamnatin jahar Kano ta hana zirga-zirgar baburan Adaidaita sahu daga karfe goma na dare
Likitoci sun yi wa dan wasan tiyata a gwiwar kafa a watan Mayu, wanda ake sa ran zai yi jinyar wata takwas.
Tsohon dan kwallon Manchester United da kuma Paris St-Germain ya koma Milan a 2020, inda ya taimaka mata lashe Serie A, karon farko tun bayan shekara 11.
Advertisements
