News
Ambaliya ta kashe aƙalla mutum takwas a Nijar
DAGA MUJAHID DANLAMI GARBA
Hukumomi a Nijar sun ce aƙalla mutum takwas sun rasa rayukansu sakamakon ambaliya da kuma ruwan sama da aka tafka a yankin kudanci da yammacin ƙasar.
Sun ce kimanin gidaje 1,300 ambaliyar ta rusa kuma mutum dubu 16 suka samu rauni.
Gwamnatin ƙasar ta buƙaci mutanen yankin da matsalar ta shafa su ƙaurace wa gidajensu.
Ko a watan satumban bara an samu irin wannan ambaliyar da ta yi sanadin mutuwar mutum sittin da kuma raba dubbai da muhallansu.
Advertisements
