DAGA MUJAHID DANLAMI GARBA
News
MDD ta buƙaci Poland ta daina nuna wa ‘yan Afirka masu neman mafaka wariya
Majalisar Ɗinkin Duniya (MDD) ta bukaci Poland ta kawo karshen wariyar da take nuna wa ‘yan ci-rani. Majalisar ta ce gwamnatin Poland na maraba da ‘yan Ukraine amma kuma sai ta garkame ‘yan asalin Gabas ta Tsakiya da Afirka da suka shiga kasar daga Belarus.
Mun kashe ‘yan bindiga 30 bayan harin da suka kai mana a Abuja – Sojin Najeriya Wakilin musamman na MDD kan ‘yan ci-rani, Felipe Gonzalez, ya ce ana rike da su cikin yanayi na tagayyara a cibiyoyi da ake jidge baki ‘yan kasashen waje ba tare da ba su damar fita ba, yayin da suke dakon takardar izinin samun mafaka.
Mista Gonzalez ya ce bai kamata a garkame yara da mutane marasa karfi ba da nuna bambanci ko fifiko tsakanin ‘yan gudun hijira. Wakilin BBC ya ce a cewar MDD, ‘yan Ukraine sama da miliyan 1.25 ne suka yi rajistar zama a kasar na wucin-gadi.
