News
Mutum 2,292 sun mutu sakamakon haɗari a tittunan Najeriya cikin wata shida’
Daga kabiru basiru fulatan
Hukumar kula da kiyayye hadura ta kasa a Najeriya ta ce mutum 2,292 ne suka mutu sakamakon haɗura 5,066 da aka samu a tittunan ƙasar daga Janairu zuwa Yunin 2022.
Jami’in wayar da kai na hukumar, Mista Bisi Kazeem, da ke sanar da haka a zantawa da manema labarai, ya ce cikin mutane 32,424 da haɗari ya ritsa da su, 16,333 sun samu munanan rauninka.
An sauyawa Ka’aba sabuwar riga da kuɗinta ya kai $6.5m
Sai dai ya ce adadin ya ɗan ja baya idan aka kwatanta da 5,320 da aka samu a 2021.
Jami’in ya ɗaura laifin haɗuran kan direbobi da ba sa tuki cikin natsu, da gudun bala’in da suke yi babu hakuri.
Ya shawarci mutane su rage tafiyar dare da sassauta gudu da mota, saboda galibi an fi samun haɗuran motoci a cikin dare.
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
