News
Bilicin ya sa na ji kamar an jefa ni a gidan yari’
Daga Muhammad Muhammad zahraddin
Wata matashiya mai suna Ellen ta bayyana irin halin tasku da ta shiga saboda yunƙurin da ta yi na sauya launin fatarta.
Matashiyar mai shekara 22 ta ce duk da ta yi nasarar sauya launin fatar tata cikin sauri, bilicin ya tsofar da ita kuma ta zama kamar ‘yar shekara 40.
Kazalika, ta ce lamarin ya saka ta ta ji kamar an kulle fatarta ne a gidan yari saboda matsalolin da ta fuskanta a lokacin da ta yi yunƙurin daina shafe-shafen.
Dole Ellen ta koma launin fatarta na asali don ta yi maganin ƙuraje da tabo-tabo da suka cika mata fuska.
Advertisements
