Wani sabon bincike ya nuna cewa kashi 58 na cutukan da ke damun al’umma suna kara tsanani ne saboda sauyin yanayi.
Jami’ar Hawaii a Amurka ta yi nazari kan makaloli 70,000 da aka rubuta, da ke da alaka da sanannun cutuka tun daga zamanin mulkin Rumawa.
Ilimi Ya Gagari Talaka, Amma ’Yan Siyasa Na Yawo A Jiragen Alfarma —Gumi
Sun kuma gano cewa sauyin yanayi na rage wa garkuwar jikin bil’adama karfi, wanda hakan ke bai wa kwayar cuta damar kara yaduwa a jikin mutum.
Kasashen duniya na fadi tashin kawo karshen matsalar dumama yanayi, da ke haifar da illoli daban daban ga bil’adama da sauran halittu.
