News
An kama injiniyan ginin da tanki ya faɗo wa mutane 2 suka mutu a Legas
Daga: Yasir sani abdullahi
Ƴan sanda a jihar Legas sun kama injiniyan da ya yi aikin ginin da wani tankin ruwa ya fado ya kashe mutane biyu a ranar Lahadi.
Kakakin rundunar ‘yan sanda a jihar, SP Benjamin Hundeyin ne ya tabbatar da cafke injiniyan a yau Talata.
Ya shawarci jama’a da su guji amfani da injiniyoyi na boge .
“Kada ku yi amfani da injiniyoyi da basu cancanta ba.
“Injiniya yana hannunmu. Ana ci gaba da gudanar da bincike.’’ Mista Hundeyin ya ce.
Ibrahim Farinloye, Ko’odinetan shiyyar Kudu maso Yamma a Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Kasa, NEMA, a jiya Litinin din da ta gabata ya bayyana cewa wani tankin ruwa da ke saman wani gini ya fado tare da kashe mutane biyu a Ladi Lak da ke yankin Bariga a Legas.
Daily Nigerian
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
