Mutanen wasu yankuna a jihar Nasarawa a arewa ta tsakiyar Najeriya sun ce zaman ɗar-ɗar da rashin tabbas sun ƙaru sakamakon yawan hare-haren ‘yan fashin daji da suka addabi jihar.
Masu yawon bude ido hudu sun mutu a hatsarin jirgin sama
A baya-bayan nan ne, gwamnan Nasarawa ya bayyana damuwa kan kwararar ‘yan fashin daji wadanda ya ce suna ƙara shiga jihar bayan an koro su daga makwabtan jihohi.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ake zaman makokin wani basarake a jihar Taraba bayan an yi masa kisan gilla a ƙarshen mako.
