Connect with us

News

An kai kwana 200 da fara yajin aikin malaman jami’o’i a Najeriya

Published

on

An sha zama teburin sulhu amma ba a daidaitawa tsakanin ASUU da gwamnatin Najeriya

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN 

 

 

 

 

 

Advertisement

 

A ranar Juma’a ne aka cika kwanaki 200 cif, da fara yajin aikin da kungiyar malaman jami’o’in Najeriya ASUU ta tsunduma.

 

A tsahon wannan lokacin dai an yi ta zama teburin sulhu tsakanin gwamnati da ASUU amma ana tashi ba tare da cimma matsaya ba.

 

Wasu daga cikin daliban da yajin aikin ya shafa, sun shaidawa BBC cewa ba su zaci lamarin zai kai tsahon wannan lokacin ba.

Advertisement

Hukumar kashe gobara ta Kano ta ceci rayuka 91, dukiya ta N24. 9m a watan Agusta

Daya daga cikinsu mai suna Ummi Musa, daliba a jami’ar Bayero da ke Kano ta ce: ”Muna tsaka da zana jarabawa aka tafi yajin aikin, daga farko gaskiya mun dan ji dadi, ganin cewa za mu samu karin makonni biyu na sake karatu.

 

Amma da aka wuce wannan lokacin sai muka gane shayi ruwa ne, lamarin nan ya janyoo mana cikas a karatu, musamman ni da ke shekara ta 4, a fannin shari’a.

 

Dan Allah gwamnati da ASUU su taimaka mana, saboda ni dai a yajin aiki aka haife ni, na girma acikinsa yau gashi har yazo kai na, idan tun daga wancan lokacin da malamai ke tafiya yajin aiki ba su yi galaba ba, kenan matakin ci gaba da yajin aiki ba zai sauya komai ba.”

Advertisement

 

Ita Shema’u ta shaidawa BBC saboda zaman gida da ya tura, har iyaye sun fara yi musu batun aure tun da karatun bai samu ba.

 

A watan Fabrairun 2022 ne dai malaman jami’o’in Najeriyar suka tafi yajin aiki, kan rashin biya musu bukatu da gwamnatin Najeriya ta yi da suka hada da alawus-alawus da karin albashi da sauransu.

 

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending