Ana sa ran sanar da ministar harkokin wajen Burtaniya, Liz Truss a matsayin shugabar jam’iyya mai mulki ta Conservative – kuma firaminista ta gaba – nan gaba a yau Litinin.
Ta jagoranci ‘yayan jam’iyyar a gangamin kada kuri’ar neman maye gurbin Boris Johnson, wanda aka tilasta wa yin murabus sakamakon tarin badakala. Mutum ɗaya da a yanzu ke hamayya da ita shi ne tsohon ministan kudi Rishi Sunak.
Yau ne za a yanke hukunci kan zaben kenya
Wakilin BBC ya ce Idan ta yi nasara, Ms Truss za ta karɓi mulkin Burtaniya a yanayi na tsadar rayuwa, matsalolin ma’aikata da ta tattalin arziki da ke neman kuno kai.
Ta alkawarta daukan matakai cikin gaggawa domin taimakawa magidanta da matsalar tsadar gas.
