Connect with us

News

Yau ne za a yanke hukunci kan zaben kenya

Published

on

DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN 

 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

An tsaurara matakan tsaro a wannan Litinin din a Kenya, yayinda ake sa ran kotun koli ta yanke hukunci kan kalubalantar sakamakon zaben shugabancin kasar da aka shigar a gabanta.

Hukumar zabe ta kasar ta bayyana mataimakin shugaban kasa, William Ruto a matsayin wanda ya yi nasara.

Advertisement

Davido ya lashe Kyauta mafi kyawun ɗan adam, Digital Artiste Awards

Sai dai abokin hamayyarsa, Raila Odinga, ya zargi cewa an yi aringizon kuri’u. Wakiliyar BBC ta ce, Odinga na son Kotu ta soke sakamakon ko kuma ta sanar da shi a matsayin wanda ya lashe zaben ko kuma ta umarci a sake gudanar da wani zabe.

Advertisement

Mista Ruto dai ya yi watsi da zarge-zarge Odinga. Mutanen biyu sun ce zasu rungumi hukunci da kotun koli za ta yanke.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending