Connect with us

News

An kama mutum takwas da laifin fashi da makamai a jahar Ondo

Published

on

NDLEA

Daga kabiru basiru fulatan

Jami’an hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA sun kama mutum takwas a wani kungurmin daji da ake zargi da aikata ta’addanci da garkuwa da mutane da kuma fashi da makami a dajin jihar Ondo.

Advertisement

An kuma samu abubuwa masu fashewa da bindiggi da harsasai da kuma tabar wiwi.

Jaridar bustan daily ta  ruwaito cewa lamarin na zuwa ne a lokacin da hukumar ta kama wani mutum dan shekara 53 mai suna Ehiarimwiam Osaromo Emmanuel da kwayar Tramadol a zauren a filin jiragen sama na Murtala Muhammed dake a Legas.

Advertisement

A sanarwar da Femi Babafemi ya aike wa manema labarai ya ce jami’an hukumar ta NDLEA sun kaddamar da samamen ne bayan wani rahoto da aka tsegunta musu, sai suka fantsama cikin kungurmin dajin Ala da ke karamar hukumar Akure ta Arewa a jihar Ondo, inda suka kama mutum takwas.d

An kama wadanda ake zargin ‘yan fashin ne a ranar Juma’a, 2 ga Satumba, 2022.

Advertisement

Abubuwan da aka kwato daga hannunsu sun hada da buhu 25 na ganyen wiwi mai nauyin kilogiram 296, da wasu abubuwa masu fashewa kamar bom guda shida da harsashin bindiga shida.

Akwai kuma babura guda hudu da layu daban daban da suke amfani da su wajen aikata ta’addanci kan mutane da suka sha tsarewa a dajin.

Advertisement

Wannan na zuwa ne a lokacin da jami’an suka kama wasu mutane masu sarrafa hodar Ibilis da ake kira Metanpethamine a Agbara dake a wajen birnin Legas.

Hukumar takuma ce ta kama wasu manyan kayan maye Wanda suke da yawan gaske

Advertisement

 

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending