A Najeriya, ana can ana zaman makoki, sakamakon rasuwar wasu mata hudu da wani jariri daya ‘yan gida daya, wadanda suka rasa rayukansu a wani hadarin kwale-kwale da ya rutsa da su a wani kogi da ke kan iyakar jihohin Jigawa da Yobe.
Wannan hadari shi ne irinsa na uku a dan tsakanin nan a jihar ta Jigawa, sakamakon tumbatsar da rafuka da koguna ke yi, saboda makeke ruwan sama da ake yi a ‘yan kwanakin nan.
Wasu ‘yan Venezuela sun bata bayan hawa wani tsauni yin addu’a
Wani magidanci mai suna Malam Bulama, mutumin garin Adiyani, wanda ya rasa mai dakinsa da matan dan uwansa uku a hadarin kwale-kwalen da ya auku yammacin jiya Laraba, ya ce abin ya firgita su da sanya tashin hankali.
Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan Najeriya a jihar Jigawa, DSP Lawal Shi’isu Adam, ya ce sun sami labarin aukuwar hadari na kwale-kwale:
Karo na uku kenan dai ana samun aukuwar irin wannan hadari na kwale-kwale a jihar ta Jigawa a makwanni biyu da suka gabata. Na farko ya auku ne a yankin karamar hukumar Miga, wanda ya yi sanadin mutuwar mutum biyu. Sai wanda ya auku a yankin karamar hukumar Gwaram, wanda ya rutsa da mutum tara, biyar suka rasa rayukansu.
