Gwamnan Jihar Sokoto kuma shugaban kungiyar gwamnonin babbar jam’iyyar adawa a Najeriya, PDP, ya ajiye mukaminsa na shugaban kungiyar.
Ya bayyana sauka daga mukamin nasa ne ranar Alhamis yayin taron Kwamitin Amintattu na jam’iyyar da ake gudanarwa a Abuja, babban birnin Najeriya.
Shugaban Kwamitin Amintattu Na PDP Ya Yi Murabus
Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, ne ya maye gurbinsa.
Tun da farko shi ma shugaban kwamitin amintattu na PDD, Santa Walid Jibrin, ya sauka daga mukaminsa.
Hakan na faurwa ne a yayin da rikicin cikin gida na jam’iyyar ke ci gaba da yin kamari.
Rikicin ya ta’azzara ne tun bayan zaben fitar da gwani na dan takarar shugaban kasa, inda aka zabi tsohon mataimakin shugaban Najeriya, Atiku Abubakar a matsayin dan takarar jam’iyyar na 2023.
Tun bayan lokacin ne mutumin da ya zo na biyu a zaben, gwamnan Jihar Ribas, Nyesom Wike, yake sukar Atiku Abubakar.
