News
Ɗan Sanata Kabiru Gaya ya rasu
DAGA YASIR SANI ABDULLAH
Sadiq Kabiru Gaya, ɗan Sanata Kabiru Gaya mai wakiltar Kano ta Kudu ya rasu.
Sadiq, lauya a hukumar kula da kadarorin Najeriya, AMCON, ya rasu ne da yammacin yau Talata a Abuja.
Kotu ta baiwa DSS damar ci gaba da tsare Mamu har tsawon kwanaki 60
Da yake tabbatar da rasuwar ta sa, Hussaini Indabawa, mai magana da yawun Sanata Gaya, ya ce an binne marigayin a yau Talata da misalin karfe 4:00 na yamma.
Sadiq, wanda ya kammala karatun fannin shari’a a Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, ya yi digiri na biyu a Jami’ar Bangor da ke Wales ta Birtaniya a shekarar 2016.
Marigayin ya bar mata ɗaya da ƴaƴa biyu.
Advertisements
