Connect with us

News

NDLEA ta kama hodar ibilis mafi girma a tarihin Nijeriya da kudinta ya kai dala miliyan 278

Published

on

NDLEA ta kama hodar ibilis mafi girma a tarihin Nijeriya da kudinta ya kai dala miliyan 278

 

Advertisement

Hukumar yaki da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa (NDLEA) ta yi nasarar kama hodar ibilis mafi girma a tarihin Nijeriya.

 

Advertisement

A ranar Litinin d ne hukumar ta sanar da fasa wani babban dakin ajiyar kaya a wani katafaren gida da ke unguwar Ikorodu a Legas.

Najeriya: Gwamnoni su ne barazana ga dimokradiyya – Ghali Na’abba

Advertisement

NDLEA ta ce nauyin hodar ya kai kimanin tan 1.8 (kilogram 1,855), wanda kudinsa ya haura dala $278, 250,000, a cewar kakakin Femi Babafemi.

 

Advertisement

An kama wasu mutane hudu da suka hada da ɗan kasar Jamaica da manajan wajen ajiye kayan, a wani samame da jami’an leken asiri suka kwashe kwanaki biyu ana gudanar da su a wurare daban-daban a Legas.

 

Advertisement

Sauran wadanda aka kama sun haɗa da Soji Jibril, mai shekaru 69, dan asalin Ibadan, Oyo; Emmanuel Chukwu 65, daga Ekwulobia, Anambra; Wasiu Akinade, mai shekaru 53, daga Ibadan, Oyo; Sunday Oguntelure, 53, daga Okitipupa, Ondo da Kelvin Smith, 42, ɗan asalin Kingston, Jamaica.

 

Advertisement

Babafemi ya yi nuni da cewa dukkansu mambobi ne na wata kungiyar masu safarar miyagun kwayoyi ta kasa da kasa da hukumar NDLEA ta ke bi tun a shekarar 2018.

 

Advertisement

An kama su ne daga otal-otal da maboyarsu a sassa daban-daban na Legas tsakanin daren Lahadi zuwa Litinin.

 

Advertisement

an kai samame ne a rumbun ajiyar, wanda ke a lamba 6 Olukuola da ke cikin jerin gidaje na Solebo a Ikorodu, a jiya Lahadi.

 

Advertisement

Ana sayar da magungunan da aka ajiye a cikin gidan ga masu siye a Turai, Asiya da sauran sassan duniya, inda a ka adana su a cikin jakunkuna na tafiya 10 da ganguna 13.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending