Sports
Man United za ta kara da City da Tottenham da Chelsea cikin Oktoba
DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN
Ranar Asabar za a ci gaba da wasannin Premier League karawar mako na takwas, bayan hutu da aka yi.
Arsenal ce ta daya a kan teburi mai tazarar maki daya tsakaninta da Manchester City mai maki iri daya da na Tottenham.
Manchester United tana tana ta biyar a kan teburin babbar gasar tamaula ta Ingila da maki 12, bayan cin wasa hudu a kakar nan.
Kungiyar da Erik ten HHag ke jan ragama ta yi canjaras biyu ta ci kwallo takwas aka zura mata takwas a raga kawo yanzu.
United za ta buga wasa tara a cikin watan na Oktoba, inda za ta yi fafata shida a Premier League da yin wasa uku a Europa League.
Cikin watan Oktoba United za ta ziyarci Manchester City a wasan hamayya ranar Lahadi 2 ga watan a karawar Premier.
Cikin wasannin Europa League da kungiyar Old Trafford za ta buga a cikin watan 10, za ta je gidan Nicosia, sannan ta karbi bakuncin kungiyar a wasa na biyu.
Ranar 27 ga watan na OOktoba, United za ta karbi bakuncin FC Sheriff a Ingila, bayan da FC Sheriff ta yi rashin nasara a gida da ci 2-0 a hannun United ranar 15 ga watan Satumba.
Wasu daga cikin wasan hamayya da United za ta buga a Premier a cikin watan nan har da wanda za ta karbi bakuncin Tottenham da wanda za ta je Chelsea.
Karawa da Newcastle United ba zai zo mata da sauki ba, gara wanda za ta yi da West Ham da Everton, wadanda ba sa kokari sosai tun fara kakar bana.
Shin wadanne wasa ne United za ta ci da wanda za ta iya barar da maki?
Wasa tara da United za ta yi cikin watan Oktoba
Premier League Lahadi 2 ga watan Oktoba
- Man City da Man Utd
Europa League Alhamis 6 ga watan Oktoba
- O Nicosia da Man Utd
Premier League Lahadi 9 ga watan OOktoba
- Everton da Man Utd
Europa League Alhamis 13 ga watan Oktoba
- Man Utd da O Nicosia
Premier League Lahadi 16 ga watan OOktoba
- Man Utd da Newcastle
Premier League Laraba 19 ga watan Oktoba
- Man Utd da Tottenham
Premier League Asabar 22 ga watan Oktoba
- Chelsea da Man Utd
Europa League Alhamis 27 ga watan Oktoba
- Man Utd da FC Sheriff
Premier League Lahadi 30 ga watan Oktoba
Man Utd da West Ham
