Connect with us

Sports

Ingila za ta kara da Jamus a wasan hamayya a Wembley

Published

on

England

DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN

Tawagar Jamus ta ziyarci Ingila, domin buga wasa na karshe a cikin rukuni a UEFA Nations League da za su fafata ranar Litinin a Wembley.

Advertisement

Ranar Juma’a Ingila ta yi rashin nasara da ci 1-0 a Italiya, Hungary ta doke Jamus har gida da ci 1-0.

Karon farko da kociyan tawagar Jamus, Hansi Flick ya yi rashin nasara a wasan da yake jan ragama.

Advertisement

Tuni Ingila ta yi kasa zuwa buga gasa mai daraja ta biyu a Nations League, bayan kasa cin wasa a karawa biyar.

Ingila ta sha kashi a wasa biyu a Hungary gida da waje har da 4-0 da aka dura mata a Wembley da wanda Italiya ta ci 1-0 da canjaras biyu.

Advertisement

Ita kuwa Jamus za ta ci gaba da buga Nations League cikin jerin kasashen da ke kan gaba a matakin farko masu buga wasannin.

Za kuma ta iya komawa ta biyu a kan teburi da zarar ta doke Ingila ranar Litinin, sannan Italiya ta yi nasara a gidan Hungary, wadda ke jan ragama.

Advertisement

Wannan karawar ta hamayya za ta bai wa kociyan Jamus damar gwada ‘yan wasa, kafin ya sanar da wadanda zai je da su kofin duniya da za a yi a Qatar a cikin watan Nuwamba.

Ingila ce tawaga ta karshe da ta ci Jamus, kafin rashin nasarar da ta yi a hannun Hungary ranar Juma’a.

Advertisement

Ingila ta ci Jamus 2-0 a Euro 2020, wadda ta kasa cin Italiya a wasan karshe a Wembley a bugun fenariti – tun daga nan kwazon Ingila yake yin baya.

Ingila wadda ta kasa cin wasa daga karawa biyar a bana ta kasa cin kwallo a wasa uku a jere, rashin kwazo mafi muni tun bayan 2000.

Advertisement

Kwallo daya ta zura a raga wadda Harry Kane ya ci a bugun fenariti da ya farke wadda Jonas Hofman ya ci Ingila suka tashi kunnen doki.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending