News
mun gaji da asara a wakilcin Jobe, muna buƙatar canji a yankinmu — Abba Ganduje
DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN
Dan takarar majalisar tarayya na ƙananan hukumomin Dawakin Tofa, Rimin Gado da Tofa, kuma dan gidan gwamnan Kano, Injiniya Umar Abdullahi Umar (Abba Ganduje), yace sun gaji da asara a wakilcin dan majalisa mai ci na yankin, wato Tijjani Abdulkadir Jobe, wanda ya shekara 16 a majalisa ba tare da abin azo a gani ba, saboda haka a yanzu suna buƙatar canji.
Nasara Radio (Amanar Talaka) ta rawaito cewa, Abba Ganduje ya bayyana haka ne bayan ya karbi wasu magoya bayan jam’iyyar NNPP a yankin, inda yace dan majalisar tasu bai iya magance matsalolin rashin aikin yi ga matasa ba, babu ayyukan mazabu, babu tallafi, sannan kuma ko a majalisar ma baya tashi ya gabatar da wani kuduri na cigaban al’umma, shi yasa har yanzu baya samun wani matsayi a majalisar, a cewarsa.
Abba Ganduje yace a yanzu kan Mage ya waye, saboda haka yake neman al’ummar yankin su bashi dama a zaɓen shekarar 2023, domin ya zama sabon wakilinsu a karkashin jam’iyyar APC, tare da alkawarin cewa zai bibiyi matsalolin kowacce karamar hukuma da mazabu na yankin, tsawon shekaru 16, da kuma yanzu domin yin abinda ya dace ga kowa.
Dan majalisa Jobe dai a yanzu shi ne yake yiwa jam’iyyar NNPP takarar dan majalisar tarayya na yankin, wanda ya baro jam’iyyar APC a watanni hudu da suka gabata, bayan tsamin alaka da suka samu da tsagin gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje.
