Connect with us

Sports

Liverpool ta sha da kyar a hannun Brighton a Anfield

Published

on

Liverpool

DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN

Liverpool da Brighton sun tashi 3-3 a wasan mako na takwas a gasar Premier League da suka fafata a Anfield ranar Asabar.

Advertisement

Liverpool, wadda take da kwantan wasa da Chelsea, ta karbi bakuncin Brighton, bayan da aka kammala wasannin kasa da kasa da aka yi a karshen mako.

Buhari zai yi wa ‘yan Najeriya jawabi ranar Asabar

Advertisement

Minti hudu da fara wasa Brighton ta ci kwallo ta hannun Leandro Trossard, sannan minti 14 tsakani ya kara na biyu.

Liverpool ta zare daya ta hannun Roberto Firmino tun kan hutu, sannan ya farke bayan da suka koma zagaye na biyu.

Advertisement

Daga nan Liverpool ta ci na uku, bayan da Adam Webster ya ci gida, sai dai kuma saura minti bakwai a tashi daga karawar Leandro Trossard ya farke, kuma na uku da ya ci wa Brighton a wasan.

Kawo yanzu Liverpool ta yi karawa 27 a Anfield ba tare da an doke ta ba, wadda ta yi nasara a fafatawa 20.

Advertisement

Wasan farko da sabon kocin Brighton Roberto De Zerbi ya ja ragama kenan, bayan maye gurbin Graham Potter, wanda ya koma aiki a Chelsea.

Masu horar da tamaula biyar a baya sun sha kashi a wasansu na farko a Anfield.

Advertisement

Da wannan sakamakon Liverpool ta hada maki 10, bayan cin wasa biyu da canjaras hudu da rashin nasara daya kenan.

Liverpool za ta fafata a wasan gaba da Rangers a Champions League, ita kuwa Brighton za ta kece raini da Tottenham a karawarta ta gaba a Premier League.27

Advertisement

BBC

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending